Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Neja na bayyana cewa wasu ‘yan fashi ?auke da bindigu sun kai farmaki fadar mai martaba Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago, da yammacin ranar Talata.
Yan fashi da makamin sun kutsa kai fadar kuma sun harbi dogarai biyu a harin wanda ake tsammanin sun biyo ?aya daga cikin hadiman fadar ne tun da farko.
An ruwaito cewa ?aya daga cikin masu yi wa fadar hidima da aka aika banki domin ya ciro ku?i ‘yan bindigan suka biyo a wata mota. Bayanai sun nuna cewa Sarki na cikin fada sa’ilin da maharan suka bu?e wuta kan mai uwa da wabi domin tsorata mutane, daga bisani suka yi awon gaba da ma?udan ku?in da ba’a san iyakarsu ba.
Tuni aka kwantar da dogarai biyu da suka ji raunuka sakamakon harin a babban Asibitin domin kulawa da lafiyarsu. Ganau, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida cewa maharan sun ci ?arfin ‘yan bangan fadar Sarkin yayin musayar wutar da ta auku.
Yayin da aka nemi jin ta bakinsa, jami’in hul?a da jama’a na rundunar ‘yan sanda reshen jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Ya ce a halin yanzun suna karban bayanai daga hadimin Masarautar a hedkwatar ‘yan sanda da ke Minna, domin tattara cikakkun bayanan abinda ya faru tun farko da ?aukar matakan da suka dace.
