Nasarar Zaben Mu: Dole Mu Yaba Gudummawar Da Wike Ya Bamu – Tinubu

Za?a??en shugaban ?asa Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike kan irin gudunmowar da ya bayar wajen tabbatar da nasararsa a za?en shugabna ?asar da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu.

Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin ?addamar da wasu ayyukan raya ?asa da gwamnan ya gudanar a jihar.

Za?a??en shugaban ?asar na ziyarar ?addamar da ayyuka ta kwana biyu da gwamnan jihar ya gayyace shi.

Tinubu ya ce ”Mai girma gwamna Nyesom Wike kai mutum ne abin dogaro”.

Ya ?ara da cewa ya fuskanci gangamin ya?in neman za?e mai ”matu?ar mai tsanani” yana mai cewa ”ba don tallafin tsare-tsare da na samu daga wasu mutane irin su Wike ba, to da samun nasara akan manyan abokan takarata irinsu Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP, zai min wahala”.

“Don haka Nyesom, ina godiya da goyon bayan da ka ba ni. ba don tallafin wasu tare-tsare da na samu ba, da nasarata ba ta tabbata ba,” in ji tsohon gwamnan na jihar Legas.

Related posts

Leave a Comment