Na Yi Farin Ciki Da Gagarumar Tarbar Dana Samu A Dawowata Najeriya – Tinubu

Rahotannin dake shigo mana daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Za?a??en shugaban ?asa Alhaji Bola Ahmed Tinubu ya ce ya yi farin cikin komawa ?asar bayan hutun mako biyar da ya yi a birnin Paris na ?asar Faransa.

Cikin wani sa?o da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Bola Tinubu ya ce ya yi matu?ar farin ciki da annashuwa kan irin gagarumar tarbar da aka yi masa a lokacin da ya sauka a filin jirgin saman Abuja babban birnin ?asar.

Za?a??en shugaban ya kuma gode wa ?imbim masoya da magoya bayansa kan irin ?aunar da ya ce suna nuna masa.

Ya ?ara da cewa yana nan a kan al?awarin da ya ?auka na samar da sabuwar Najeriya.

Za?a??en shugaban ?asar ya kuma ce yana cikin ?oshin lafiya sa?anin jita-jitar da ake ya?awa cewa yana cikin halin rashin lafiya.

Jama’a dai sun yi ta rade-radin cewa zababben Shugabagann ya tafi waje ne domin neman lafiya, inda aka yi ta surutai akan rashin ganinsa a lokacin gudanar da sallar idi a masallatan idi dake fa?in ?asar.

Related posts

Leave a Comment