Mun Damu Da Halin Da ‘Yan Najeriya Ke Ciki A Sudan – Gwamnatin Tarayya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta ce jami’anta na yin iya bakin-?o?arinsu tare da ha?in gwiwwar ofishin jakandancin kasar da ke Sudan, da gwamnatocin ?asashen Sudan da Habasha domin tabbatar da kare lafiyar dubban ‘yan ?asar da ke Sudan.

Cikin wani sa?o da mai magana da yawun shugaban Najeriya Mallam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya ce ministan harkokin wajen ?asar Geoffrey Onyeama ne ke jagorantar shirin wanda zai taimaka wajen fitar da ‘yan ?asar daga wuraren da ake rikici a ?asar Sudan.

Haka kuma ofishin jakadancin ?asar da ke Khartoum ya fitar da wata sanarwa wadda a cikin, ofishin ke kiran ?aliban ?asar da ke Sudan da su yi watsi da wasu bayanai da ?ungiyar ?aliban ?asar reshen Sudan ke ya?awa, wanda ke kiran ?aliban da su taru a wasu wurare uku domin kwashe su zuwa Najeriya.

Sanarwar ta yi kira ga ?aliban da su kwantar da hankalinsu, sannan su zauna a gidajensu, yayin da ofishin jakadancin ya ce yana ?o?arin ganin ya kammala shirye-shiryen fara kwaso ?aliban.

Ofishin jakandanci ya ce yana shaida wa ?aliban cewa kwanciyar hankali da lafiyarsu shi ne baban damuwarsa.

Related posts

Leave a Comment