Bauchi: ‘Yan Jarida Sun Sha Alwashin Fadarkawa Kan Kiwon Lafiya

Daga Adamu Shehu Bauchi

Yan’jarida masu dauko rahottanin kiwon lafiya a jihar Bauchi sunsha alwashin sauke nauyin dake rataye a wuyansu na fadakar da al’umma kan ababen da suka shafi matsalolin samar da ingantachiyar lafiya a matakai daban daban a fadin jihar.

Sunsha wan nan alwashin ne yayin wani taron tattaunawa na kwana daya tare da hukumar taimakekeniyar lafiya ta jihar Bauchi

Da take tsokaci a lokacin taron Shugaban masu dauko rahottanin kiwon lafiya ta jihar Elizabeth Carr, tace sun kirayi shuwagabanin gidajen radiyo na al’umma dasu fahimci muhimmanci taimakekeniyar lafiya domin fadakar da mutanen karkara kan wan nan shiri da gwamnatin jihar ta fara a watannin baya.

Kana tace sun dukufa domin sanar da al’ummar jihar baki daya ta hanyar rubuta labarai da sanarwa a fannonin sadarwa da ilmantarwa

Tun a farko kwamishinan kiwon lafiya na jihar wanda babban sakataren ma’aikatar ya wakilta a wajen taron, Aliyu Babayo yace Yan’jarida na da babban gudumuwar da zasu bayar ta wajen zakulo tambayoyi da amsoshin al’umma kan hidimar kiwon lafiya, a yankunansu kana su watsa shi a kafefen labarai don tabbatar da sakonnin mahukunta ya isa zuwa inda ake bukatar shi.

Dokta Mansur Dada Shugaban Shirin taimakekeniyar lafiya, a lokacin taron yayi karin haske kan ayyukan su, inda yace, “shiri ne wanda yake da matukar muhimmanci domin rage radadin talauci don jama’a su samu daman samun ziyartar asibitochi don samun lafiya ingantacce”

Ya kara da cewa, “jama su fahimci samunsu na yau da kullon kafin su game ta yadda zasu ci moriyar wan nan shiri baki daya, don yace kudi kalilan mtum zai he yayi ragista a offishin hukumar, don chin gajiyar shirin taimakekeniyar”

Daga ba karshe masana harkokin kiwon lafiya sun gudanar da jawabai na karawa juna sani da hankaltar da manema labarai kan bin diddigi domin aikin al’umma dake rataye a wuyan su na fadakarwa da ilmantarwa.

Related posts

Leave a Comment