2023: EFCC Za Ta Tura Jami’anta Domin Sa Ido Kan Zabe

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta ce za ta tura jami’anta zuwa jihohi 36 na fa?in Najeriya don sa ido a za?en ?asar da za a gudanar.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na twita, shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa, ya hori jami’an da su sanya bu?atar ?asa a farko da kuma nuna ?warewa yayin gudanar da aikinsu.

“An tura ku ne don ku je ku yi wa ?asa aiki, a don haka, ya kamata ku kasance yanda ake bukata ta hanyar nuna ?warewa da kuma aiki da dokokin hukumar,” in ji Bawa.

Ya ?ara da cewa suna da alhakin tabbatar da cewa ba a yi magu?i ba a wannan za?e, musamman ma bai wa masu za?e ku?i.

Ya ce akwai bu?atar su yi abin da ya kamata saboda idon duniya ya koma kan Najeriya na ganin an gudanar da za?e cikin gaskiya da lumana.

Related posts

Leave a Comment