Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi shelar cewa an kashe zaratan jami’an ta shida, yayin da wasu shida kuma an neme su an rasa, bayan da ‘yan bindiga suka yi masu kwanton-?auna a Jihar Delta.
Kakakin Ya?a Labaran Hedikwatar ‘Yan Sanda ta ?asa, a Abuja, Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana haka cikin wata sanarwar da ya buga a shafin tiwita, wato X.
A ranar Asabar ya saki sanarwar, amma bai bayyana ranar da aka kashe ‘yan sandan da kuma ranar da su ma wa?anda aka rasa inda su ke ?in suka ?ata ba.
Adejobi ya ce ‘yan sandan da kashe da wa?anda ake nema ?in sun je ne domin binciken yadda wasu abokan aikin su uku suka ?ace a cikin Dajin Ohoro, cikin Jihar Delta.
A can cikin dajin ne ‘yan bindiga suka yi masu kwanton-?auna, suka kashe har da insifeto biyu, sajen hu?u, yayin da ake neman insifeto hu?u, sajen biyu har yau shiru, babu labarin su.
