2023: INEC Ta Gayyaci ‘Yan Takara Sa Hannun Amincewa Da Gudanar Zabe Cikin Sauki

Shugaban Hukumar Za?e na ?asa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce dukkan ‘yan takarar shugaban ?asa za su bayyana a ranar Laraba, domin su sa hannu kan yarjejeniyar amincewar yarda a gudanar da za?e lami lafiya, ba tare da tashin hankali ba.

Yakubu ya bayyana haka a lokacin ganawar sa da ‘yan jarida, bayan ya kai ziyara Makarantar Sakandire ta Garki, Abuja, inda ake bayar da horo ga Masu Sa-ido Kan Jami’an Za?e (SPO).

Shugaban na INEC ya kuma kai irin wannan ziyarar a Cibiyar Taro ta ?asa-da-?asa (ICC), inda a ce a can ne jihohi za su ri?a aikawa da sakamakon za?e ana tattarawa. Daga ?arshe kuma a can ne shugaban na INEC zai bayyana ?an takarar da ya yi nasara, tare da sakamakon da kowane ?an takara ya samu.

Yakubu ya ce haka kuma ICC zai kasance Cibiyar Ya?a Labarai.

Haka kuma Yakubu ya ce INEC ba za ta fuskanci matsalar ?arancin ku?i ba, bisa dogaro da al?awarin da Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya yi wa shugaban na INEC, a lokacin da ya ziyarce shi.

Ya ce yawancin ayyukan da INEC za ta biya ma’aikata duk tura masu a asusun ajiyar su za ta yi.

Da ya ke magana kan ?alubalen tsaro, ya ce wannan aikin jami’an tsaron ?asa ne, kuma sun yi alkawarin babu wani gagararren da za’a bari ya haifar wa za?en 2023 da cikas.

Ya ce Kwamitin Wanzar da Zaman Lafiya ba ?asa da ke ?ar?ashin Tsohon Shugaban ?asa, Abdulsalami Abubakar ne zai shirya taron rattaba hannun amincewar da ‘yan takarar za su yi a ranar Laraba, 22 ga Fabrairu, 2023, a Cibiyar Taruka ta ?asa-da-?asa (ICC), a Abuja.

Ya ce INEC ta kammala shirye-shiryen gudanar da za?en 2023 a cikin kwanciyar hankali.

Related posts

Leave a Comment