Tsadar Rayuwa: A Kara Hakuri Ina Sane Da Halin Da Ake Ciki – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya godewa ‘yan Najeriya bisa zabensa da suka yi ya yi mulki a kasar har sau biyu; daga 2015 zuwa 2023.

Shugaban ya bayyana cewa, ya yaba da kokarin ‘yan kasar bisa wannan karimci da suka ba shi na damar shugabantarsu.

Idan baku manta ba, saura kwanaki shida kacal a yi zabe a Najeriya, kuma shugaban kasa Buhari na da dan takarar da jam’iyyarsa ta tsayar don maye gurbinsa.

Da yake yiwa ‘yan Najeriya bayanan godiya a shafinsa na Facebook, Buhari ya ce: “‘Yan uwana ‘yan Najeriya, ina so na yi amfani da wannan damar har ila yau don gode muku bisa zaba ta da kuka yi na zama shugaban kasa har sau biyu.” Ina sane da halin kuncin da kuke ciki, cewar Buhar.

i A bangare guda, shugaban kasan ya ba ‘yan Najeriya hakuri bisa halin da ake ciki bisa sabbin ka’idojin da gwamnatinsa ta samar. A cewarsa: “Daga karshe, ina so na tabbatar muku cewa ina sane daram da halin kunci da kuke fuskanta saboda wasu ka’idojin da gwamnati ta kawo wadanda aka yi su da nufin kawo ci gaba ga kasar.

“Ina rokonku da kara hakuri yayin da muke daukar matakan da suka dace don saukake wadannan wahalhalu. Idan Allah ya yarda, akwai harke a nan gaba kadan.

Related posts

Leave a Comment