Kaduna: Uba Sani Ya Yi Alkawarin Tallafawa Mata Ta Fuskar Koyar Da Sana’o’i

Dan takarar gwaman jihar Kaduna a jamiyyar APC Sanata Uba Sani ya yi alkawarin ci gaba da koyar da mata sana’oin hannu don su zamo masu dogaro da kansu idan aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar a 2023.

Ya yi nuni da cewa, gwamnatin jihar ce tilo a kasar nan da ta ke yin tafiya da mata, inda ya ce, in ya kai ga gaci, zai tabbatar da nada mata a cikin gwamnatin sa da kuma tallafa wa kasuwanci su.

Dan majalisar ya bayyana hakan ne a yayin da ya gana da alummar karamar hukumar Kajuru a lokacin da yaje gangamin yakin neman zabensa da mataimakiyar sa Haj Hadiza Sabuwa Balarabe.

Uba kuma yi alkawarin taimaka wa jama’an tsaro da ke gudanar da da ayyukan yakar yan bindiga daji da ke aikata ta’asar su a wasu sasaan jihar.

Ya ce, akwai bukatar jihar da kananan hukomomin da ke jihar da kuma sauran dai daikun jama’ar da ke a jihar, suma su bayar da ta su gudunmawar don a kara tabbatar da tsaro a jihar.

Ya yaba wa gwamnan jihar Nasir Ahmed El-rufai akan samar da kayan aikin ga jami’an soji don su yaki yan bindigar inda ya ce, hakan ya taimaka matuka wajen dawo da zaman lafiya a jihar, mussman idan aka yi la’akari da yadda dakarun suke ci gaba fatattakar yan ta’addar daga mafakar su.

Uba ya kuma kaddamar da aikin dakin shan magani na matakain farko da aka gyra aka kuma sanya kayan aiki.

Har ila yau, a jawabinsa a fadar Etsu Chikun Sanata Uba ya yi alkawarin ci gaba da gudanar da ganawar da alummar gari musamman don wanzar da tsare-tsaren gwamnatinsa in Allah ya bashi nasara.

Ya yi nuni da cewa, nadin da aka yiwa Etsu na Chukun hakan ya kara tabbatar sa zaman lafiya a yankin, inda ya ce, rikice-rikicen addini da na kabilanci a yankin, sun ragu matuka.

Ya ci gaba cewa, in har aka zabe shi, gwamnatin sa za ta mayar da hankali wajen kammala ayyukan hanoyi a Chikun tare da kuma kara kirkiro da wasu sabbi .

Bugu da kari, Sanata Uba a jawabin da ya yiwa dandazon magoya bayansa a Sabon Tasha ya bukace su da su zabi APC tun daga sama har kasa a zaben 2023.

Related posts

Leave a Comment