Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Wa El-Rufa’i Martani Kan Tinubu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin Tarayya ta mayar da martani kan zarge-zargen da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi na cewa ”wasu mutane” a fadar shugaban ?asar na ?o?arin da?ile nasarar ?an takarar shugaban ?asar na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.

El-Rufai ya yi zargin ne a wata hira da ya yi da gidan talbijin na Channels TV ranar Laraba, inda ya ce ”na yi imanin cewa akwai wasu a fadar shugaban asar da suke so mu fai zae, saboda ba su samu yadda suke so ba”

”Suna da nasu ?an takarar, amma bai yi nasara a za?en fidda gwani ba, ina ganin har yanzu suna so mu fa?i za?e, kuma suna ra?e wa da burin shugaban ?asa na ganin ya yi duk wani abu da yake jin daidai ne”, in ji El-rufai.

To sai dai ministan ya?a labaran ?asar Lai Mohammed, ya mayar da martani a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi jim-ka?an bayan kammala taron majalisar zartarwar ?asar, da shugaban ?asar Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Lai Mohammed ya sake jajjada matsayin shugaban ?asar na cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen tabbatar da gudanar da sahihi kuma amintaccen za?e a ?asar ba tare da yi wa wani alfarma ko da?ile wani ba.

Ya ?ara da cewa in ma akwai wanda yake yi wa wani ?an takarar zagon ?asa, to su a hukumace ba su san shi ba.

Related posts

Leave a Comment