Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya bu?aci shugabannin ?ungiyar Fulani ta Miyetti Allah da su taimaka wa gwamnatin tarayya wajen magance matsalar tsaron da ?asar ke fuskanta.
Yayin da yake magana a Abuja babban birnin tarayya lokacin bikin rantsar da sabbin shugabannin ?ungiyar, sarkin Musulmin ya ce al’ummar Fulani makiyaya masu son zaman lafiya ne da kaunar juna.
Muhammad Sa’ad Abubakar III wanda shi ne shugaban Majalisar ?oli ta Addinin Musulunci, ya yi kira ga sabbin shugabannin ?ungiyar da su yi ?o?arin taimaka wa gwamnati wajen magance matsalar tsaro da ?asar ke fuskanta.
Najeriya musamman yankin Arewa maso yamma na fuskantar gagarumar matsala ta rashin tsaro da ake dangatashi ga Fulani makiyaya masu ikirarin ?aukar fansa akan abin da suka kira cutar dasu da ake yi a yankin.
Matsalar tsaron ta yi sanadiyar mutuwar mutane masu yawa da tursasa jama’a da dama barin muhallin su a yankin gami da tayar da ?auyuka masu yawa a yankin.
