Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ya umarci kwamashinonin rundunar na jihohi da su ?addamar da tsarin ba da kariya ga ayyukan babban za?e na 2023 da ke ?aratowa.
Kazalika, babban sufeton ya umarce su da su tabbatar da tura dakarun kwantar da tarzoma zuwa wuraren da suka dace.
“Sufeto janar ya bayyana cewa tashin hankali da kalaman ?iyayya da barazana da rashin jimuri da ya?a labaran ?arya da tsattsauran ra’ayin siyasa baraza ne ga dimokura?iyyarmu da tsaron ?asa,” a cewar sanarwar da Kakakin ‘Yan Sanda na ?asa Olumuyiwa Adejobi ya fitar a yau Lahadi.
Tsarin ya ?unshi yin aiki tare da sauran jami’an tsaro na ?asar da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki don lalubo hanyoyin tsaurara tsaro a ofisoshin hukumar za?e ta INEC.
