Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El Rufa’i da Bello Matawalle na jihar Zamfara, da Simon Lalong na jihar Filato, sun ziyarci ?an takarar shugaban ?asa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a Abuja.
An ruwaito cewa gwamnonin guda uku sun gana da Tinubu da ?an takarar mataimakin shugaban kasa, Sanata ?ashin Shettima.
Sauran jiga-jigan jam’iyya mai mulki da suka halarcu taron sun ha?a da Sakataren APC na ?asa, Iyiola Omisore, da tsohon shugaban jam’iyya na ?asa, kwamaret Adams Oshiomhole.
Duk da ba bu wani cikakken bayani kan abin da suka tattauna, ammma ana ganin ziyarar ba zata rasa nasaba da shirye-shiryen babban za?en 2023 da ke tafe ba.
