Bullar Sabuwar Cuta: NCDC Ta Shiga Bincike

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Hukumar NCDC mai ya?i da cutuka masu ya?uwa ta ce ta ?addamar da bincike kan wata ba?uwar cuta da ta ?ulla a Jihar Delta da ke kudancin ?asar.

Rahotanni na cewa a makon da ya gabata wani ?alibi ya mutu tare da kwantar da wasu tara a asibiti sakamakon cutar a yankin Boji-Boji na ?aramar Hukumar Ika ta Arewa-maso-Gabas.

Cikin wani sa?o da ta wallafa a shafinta na Twitter, NCDC ta ce tana sane da wata cuta da aka ce ta ?arke tsakanin ?aliban sakandare.

NCDC ta ?ara da cewa tana ha?a hannu da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, da kuma Ma’aikatar Lafiya ta Delta.

Related posts

Leave a Comment