Abuja: NDLEA Ta Cafke Manyan Dillalan Hodar Iblis

A?alla mutum takwas ne hukumar NDLEA mai ya?i da shan miyagun ?wayoyi a Najeriya ta kama kan zargin safarar hodar-ibilis ko kuma koken.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Asabar, kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya ce wasu daga cikin mutanen da aka kama na yun?urin fita da ?wayoyin ne, yayin da wasu kuma ke shiga da su Najeriya.

An kama su ne a filayen jirgin sama na Abuja da Legas da Enugu, kuma biyu daga cikinsu mata ne.

?aya daga cikinsu mai suna Okwo Paul Okechukwu, an kama shi ranar 17 ga watan Yuli bayan ya ha?iye ledar koken har 76 a cikinsa, wa?anda daga baya ya yi kashinsu a ofishin hukumar.

Related posts

Leave a Comment