Babbar Kotun Indiya ta ladabtar da tsohuwar kakakin jam’iyya mai mulki bayan wasu furucinta kan Annabi Muhammad ya haifar da ce-ce-ku-ce a ?asar.
Kotun ta fa?awa Nupur Sharma cewa “harshenta mara linzami ya kunna wutar rikici a ilahirin ?asar”.
Kalamanta a lokacin wata muhawara da aka haska a gidan Talabijin sun haifar da rikici a wasu sassan ?asar da tunzura ?asashen Musulmi da dama aike bukatar garga?i mai tsauri kan Indiya.
Kotu ta bu?aci ta bayyana gaban Talabijin domin neman gafarar ‘yan ?asar baki ?aya.
Ms Sharma ta ro?i kotu ta hana bincike-binciken da take fuskanta a sassa daban-daban na ?asar.
Kotu ta yi watsi da bukatar, tana mai cewa ” wannan korafi ne cikin rashin ?a’a, kuma kotunan ?asar sun fi karfinta.”
Lauyanta ya shaidawa kotu cewa ya nemi afuwa da kuma janye kalamanta.
Amma masu shari’a na cewa “ta makara waje janye kalaman nata, kuma tayi hakan ne bisa shara?i, tana cewa idan hakan ya ?ata ran wasu”.
Kotun ta ce kasancewa mai magana da yawun jam’iyya, bai ba wa mutum lasisi fa?in din abin da yake so ba domin ba?anta ran mutane.
Ms Sharma ita ce mai magana a madadin jam’iyyar BJP mai mulki lokacin da ta yi wa?annan kalamai.
An dakatar da ita daga jam’iyyar bayan ?asashen musulmi da dama ciki harda UAE, da Saudiyya da Qatar da Iran sun shigar da korafinsu na adawa a hukumance cikin diflomasiyya.
Batun ya kasance gagarumin barazana ga yunkurin Indiya na inganta huldar diflomasiyarta da ke neman sukurkucewa da wadannan ?asashe.
Kotun ta kuma fahimci cewa “hakan da ta aikata shi ya kai ga matsalar da aka samu a Udaipur”.
Jihar da ke arewacin Rajasthan na cikin yanayi na zama ?ar-?ar bayan wasu maza biyu Musulmai sun fille kan wani tela Hindu.
Sun na?i lokacin da suke aikata hakan da ?aura bidiyon a intanet, suna cewa harin martani ne na nuna goyon-bayan Kanhaiya Lal ga Ms Sharma a shafukan sada zumunta.
