BASHIR ADAMU, JALINGO
Wani Dattijo mai son cigaban Kasannan, Alhaji Isa Tafida Mafindi, Yariman Muri, yace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi dai-dai da yace abashi dama ya fitar da magajinsa a Jam’iyyar APC.
A cewar Isa Tafida Mafindi, ko shakka babu, jigo a Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya taka rawa matuka wurin samun nasaran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Zaben shekarata 2015.
Mafindi na mai cewa tuni Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gama sakama Jigo Bola Ahmed Tinubu wahal-halun daya sha ta hanyar barinshi ya kawo wasu muhimman mukamai da suka hada da Mataimakin Shugaban Kasa, wasu Ministoci, Daraktoci da Chairmomin gudanarwa a wasu Hukumomin Kasa da dai sauransu.
A cewan Dattijo Mafindi ko kadan bai kamata Mulkin Kasannan Ya karkata Kudu ba, ganin yawancin Manyan Mukamai kimanin kaso 70 zuwa 80 da Shugaban Kasa ya bayar, yayi hakanne da nufin saka musu, kana ya shawarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da yayi tsayin daka akan wannan manufa nashi, domin cigaban Al’umman Kasannan baki daya.
