Damfara: EFCC Ta Damke Tsohon Gwamnan Zamfara

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar jami’an hukumar EFCC sun damke tsohon Gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari, bayan an gano ya na da hannu dumu-dumu wajen badakalar naira biliyan 80 na Akanta Janar Ahmed Idris.

EFCC ta bayyana cewa ta kama Yari a gidan sa da ke Abuja, bayan bincike ya nuna cewa ya jidi naira kusan biliyan 20 daga cikin naira biliyan 80 ?in da EFCC ke nema wajen Akanta Janar.

EFCC dai ta kama Ahmed Idris ne cikin makon shekaranjiya, bisa zargin karkatar da naira biliyan 80 da aka ba shi amanar ajiyewa cikin ku?a?en Najeriya.

An dam?i Yari a ranar Lahadi a Abuja, kwanaki ka?an bayan ya ci za?en fidda-gwanin Sanatan APC na Zamfara ta Yamma ba hamayya.

A cikin 2021 EFCC ta sha kama Yari bisa binciken yadda ya karkatar da biliyoyin ku?a?e, wato wasu daban ba wa?annan biliyan 20 da ake magana a yanzu ba.

Ya yi Gwamnan Jihar Zamfara daga 2007 zuwa 2019.

Related posts

Leave a Comment