EFCC Ta Wuce Gona Da Iri Wajen Kama Okorocha – Malami

Antoni-janar na tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, ya umarci hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC da ta dakata da tuhumar tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, wanda a baya hukumar ta kama karfi da yaji a gidansa ranar Talata.

Umarnin da Malami ya bayar na dakatar da tuhumar yazo ne a wata wasikar da Abdulrasheed Bawa, shugaban EFCC ya fitar a ranar 21 ga watan Afirilu, a wani martani kan wasu korafe-korafe da Ola Olanioekun, lauyan Okorocha ya shigar.

Kamar yadda wasikar da Malami ya sa hannu, Olanipekun, babban lauyan ya zargi EFCC da karya dokar kotu yayin tuhumar gami da kama tsohon gwamnan jihar Imo. A korafin da Okorocha ya shigar, AGF ya janyoo hankalin EFCC a kan umarnin kotun da babbar kotun tarayya ta Port-Harcourt ta bayar, a shekarar da ta gaba.

Malami ya cigaba da cewa, bincike gami da tuhumar Okorocha ya ci karo da hakkinsa na damar sauraro yadda ya dace karkashin sashi na 6(6) a kundin tsarin shari’a na shekarar 1999.

A baya, an gano yadda EFCC da tawagar lauyoyin Okorocha suka dade suna dauki ba dadi a kan hukuncin kotun Port Harcourt. Olanipekun, lauyan Okorocha ya shigar da korafi ga kotu, inda ya zargi EFCC da karya dokar kotu, wacce ta umarci hukumar da ta sakarwa sanatan fasfo?insa.

Bayan kin bin umarnin kotun da hukumar tayi, Okorocha ya sake shigar da kara a wannan dai kotun don tsare masa hakkinsa na bil’adama, wanda ya ce an take. Olanipekun ya cigaba da shaida wa kotu duk da umarnin da ta bada, EFCC ta yi kunnen uwar shegu game da sakin fasfodin wanda ake karewa da sauran takardun tafiyarsa, inda ya kara da cewa, “Alamu na nuna yadda babu wata shari’a da aka yi a nan.”

Sai dai lauyan EFCC, N A Dodo ya musanta karya dokar kotun da ake zargin EFCC tayi, inda ya ce hukumar ta kira Okorocha a waya tare da shaida masa ya zo ya amshi fasfo?insa da sauran takardun tafiyarsa, amma bai zo ba.

Daga bisani hukumar ta damko shi da karfi da yaji a ranar Talata bayan daukar awanni 6 suna dakonsa a gidansa na unguwar Maitama dake babban birnin tarayya Abuja.

Related posts

Leave a Comment