A ziyarar da ya kai Jihar Katsina mataimakin shugaban ?asa Farfesa Yemi Osinbajo ya samu gagarumar tarba daga Katsinawa inda ya kai ziyarar ban girma ga fadar mai martaba Sarkin Katsina Abdulmuminu Kabir Usman.
Sarkin ya bayyana goyon bayan shi ga Osinbajo tare da addu’ar samun nasara a babban za?e dake tafe na shekarar 2023.
Bayan nan jirgin ya?in neman za?en Osinbajo ya shilla JIhar Yobe inda ya ziyarci fadar Sarkin Damaturu, Hashimi II El-Kanemi, domin gaisuwa da neman tubarraki akan bukatarsa ta neman shugabancin kasa.
Da yake maida jawabi Sarkin na Damaturur ya ce Masarautar za ta goyi bayan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo tare da yin addu’a a kan Allah Ya sa ya zama shugaban ?asa a 2023.
Basaraken ya ce ziyarar da mataimakin shugaban kasar ya kai fadar wata alama ce da ke nuna girmamawar da ya ke da ita ga masarautun gargajiya.
“Abin da muke sa rai shi ne ci gaba; don ?ora wa da ga inda a ka tsaya, kuma da ga nan ne za ku ci gaba.
