Za A Kara Farashin Kudin Kiran Waya A Najeriya

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta ?asa ta ce ta samu takarda daga ?ungiyar kamfanonin sadarwa na ?asar na neman yin ?arin ku?in kiran waya da kuma data sakamakon tsadar gudanar da ayyukansu.

Rahotanni sun ce takardar da ?ungiyar ta gabatar na neman yin ?arin kashi 40 cikin 100 na farashin kiran waya da aika sa?o.

Kamfanonin na son yin ?arin ne na kira daga N6.4 zuwa N8.95, farashin aika sa?o kuma zai koma N5.61 maimakon N4.

Hauhawan farashi a Najeriya kusan ya shafi ko wane ?angare, yayin da masu saye da sayarwa suka fi jin tasirinsa.

Ta?ar?arewar darajar naira ya ?ara haifar da tsadar kayayyakin, musamman a ?asar da ta dogara da shigo da kayayyakin bu?atu na yau da kullum daga waje.

Related posts

Leave a Comment