Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar EFCC da ke ya?i da cin hanci da rashawa ta ce tana sa ido kan tushen ku?a?en da ake amfani da su wajen sayen fom ?in takara na jam’iyyun siyasa.
Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ne ya bayyana haka a wata hira da kafar talabijin ta Channels ta yi da shi a ranar Juma’a.
Ya ce hukumarsa ta EFCC na ha?a kai tare da hukumar za?e mai zaman kanta INEC domin gano inda aka samo ku?a?en da ?an siyasa ke sayen fom.
“Gaskiya ku?i ne masu yawa, domin za ka iya kwashe tsawon rayuwarka kafin ka tara naira miliyan 40 ko kuma miliyan 100,” in ji shi.
Shugaban na EFCC ya ce hukumar za ta yi ?o?arin tabbatar da masu “kashi a gindi” ba su kai ga samun mu?aman shugabanci a Najeriya ba.
Bawa ya ce “EFCC na aiki a ?oye domin banka?o irin wa?annan marasa gaskiya.”
Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya tana sayar da fom na shugaban ?asa kan farashin naira miliyan 100 yayin da babbar jam’iyyar adawa ta PDP ke sayar da nata kan naira miliyan 41.
Ya zuwa yanzu kusan mutum 20 ne suka saye fom ?in APC na shugaban ?asa yayin da a?alla mutum 17 suka sayi na PDP.
