Shugabancin Kasa: Amaechi Ya Fi Kowa Cancanta – Sarkin Dutse

Rahotannin dake shigo mana daga Dutse babban birnin jihar Jigawa na bayyana cewar Mai martaba sarkin Dutse, Nuhu Mohammadu Sanusi, ya goyi bayan takarar ministan sufuri, Rotimi Amaechi a babban zaben shugaban kasa na 2023 dake tafe.

Da yake magana a yayin da ya karbi bakuncin Amaechi a fadarsa da ke garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa, a ranar Talata, Sanusi ya bayyana Amaechi a matsayin mutum mai gaskiya.

Sarkin ya ce Amaechi na da dukkanin abun da kasar ke bukata daga shugaba. “Shi mutum ne mai gaskiya, kuma komai za ka fada game da shi, ba za ka taba sauya gaskiyar cewa shi mutum ne mai gaskiya ba.

Mutum ne mai kwarin gwiwa. A duk inda ka gan sa za ka san cewa shine abun da ake kira da cikakken karfin gwiwa. “Wadannan sune abun da ake so daga shugaba. Wadannan sune abubuwan da muke bukata a jagora musamman a yau, mutane masu kwarin gwiwa, wadanda za su iya fuskantar gaskiya da kalubale.

Yana da juriya. Juriyarsa zan sake fada maku cewa, idan Amaechi na son cimma wani abu, ta kowanr hali, zai nemi hanyar ganin ya same shi, saboda shi mai sadarwa ne.

“Wannan ne dalilin da yasa na mara masa baya. Ina mutunta shi sosai kuma ina da kwarin gwiwa a kansa. Ya cancanta sosai, kasancewarsa kakakin majalisa sau biyu. Shi ya fi cancanta.” Amaechi ya mutunta Musulmai a lokacin da yake matsayin gwamnan Ribas.

Basaraken ya ce Amaechi ya samawa Musulmai da Kirista wuri a Ribas a lokacin da yake a matsayin gwamnan jihar, “A Najeriya, al’amura na kabilanci, siyasa da sauran su kan dauke mana hankali a kodayaushe amma anan ga wani dan Najeriya da na sani, kuma Amaechi dan Najeriya ne na gaskiya wanda bashi da kabilanci.

Related posts

Leave a Comment