Kakar Zabe: Ayyana Takarar Osinbajo Ta Haifar Da Rudani

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Mutane da dama ba su yi farin ciki da ayyana takarar mataimakin shugaban kasa Osinbajo bane saboda manufofin jam’iyyun siyasansu ko kuma wasu abubuwa da suka yi imani dasu.

Masu kiyasi sun ce takarar Farfesa Yemi Osinbajo zata raba kawunan gwamnonin Kudu maso yamma da na jam’iyya mai mulki APC, musamman damar samar da shugaban kasa daga kudu.

Daga martanin mutane a kafafan sada zumuntar zamani, za a iya gano yadda mutane da dama ba su yi farin cikin da bayyana bukatar Osinbajo ba.

1. Magoya bayan Asiwajo Ahmed Tinubu. 2. ‘Yan Najeriyan da suka yi imani da cewa mataimakin shugaban kasan bai cancanta ba. 3.Magoya bayan ‘yan takarkarin kudu maso gabas. 4. Wadanda ke kallon Osinbajo a matsayin wanda ke bayyana addininsa.

Related posts

Leave a Comment