Gwamnatin Tarayya Ta Raba Wa Tsoffin ‘Yan Wasan Super Eagles Gidaje

Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola ya gabatar da takardun gidaje ga tsoffin ?an wasan ?wallon kafa na Super Eagles da gwamnatin tarayya ta yi masu al?awali.

Hotunan da ma’aikatar ayyuka da gidaje ta wallafa a Twitter sun nuna lokacin da ?an wasan ke karbar takardun gidajen hannun Fashola a ranar Juma’a.

An ba tawagar Super Eagles da suka buga wa ?asar wasa a 1994 gidajen ne bayan shekara 28 da gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha ta yi masu al?awali lokacin da ?an wasan suka lashe kofin Afirka a Tunisia.

Ana ganin cika alkawarin da gwamnatin Buhari ta yi zai kara sanya kwazo da karsashi ga ‘yan wasan kungiyar na yanzu wajen kare martabar ?ungiyar.

Related posts

Leave a Comment