2023: Osinbajo Zai Ayyana Shiga Takarar Shugabancin Kasa

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mataimakin shugaban ?asa, Farfesa Yemi Osinbajo, a wasu ?an kwanaki masu zuwa zai ayyana shiga takarar shugaban ?asa a hukumance ?ar?ashin inuwar jam’iyyar APC.

Hakan na zuwa ne bayan jita-jita ta yawaita da kuma musanta lamarin da hadimansa da abokanansa suka yi. An jima ana ya?a jita-jitar cewa Mataimakin shugaban zai nemi takarar Kujerar Shugabancin kasa a Najeriya a babban za?en 2023 dake tafe.

A baya an ya?a cewa Farfesa Osinbajo zai fito da kudirin dake zuciyarsa na takara a ranar 7 ga watan Afrilu , amma kuma hakan bai faru ba.

A halin yanzu, wata majiya a cikin fadar shugaban ?asa, ranar Alhamis ta ambato cewa shiri ya kammala domin ayyana shiga takarar mataimakin shugaban ?asa.

Majiyar daga Aso Rock ta yi wannan jawabi ne bisa shara?in ?oye bayananta, inda ta ce, “Zai bayyana shiga tseren cikin yan kwanaki ?alilan masu zuwa.”

Tuni dai ?ungiyoyin dake goyon bayan mataimakin shugaban suka tsara Fastoci, suka manna su a wurare daban-daban na gwamnati a babban birnin tarayya Abuja.

Related posts

Leave a Comment