Tsigeni A Limanci Bai Girgiza Ni Ba – Sheikh Nuru Khalid

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon Limamin masallacin Apo da ke Abuja, Sheikh Nuru Khalid, ya ce korarsa da kwamitin masallacin ya yi, wata sadaukarwa ce da ya zama dole ya yi domin talakawan da ke cikin wahala da kuma fadin gaskiya ga masu mulki.

Sheikh Khalid ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Litinin da daddare, inda ya kara da cewa korar tasa bai girgiza shi ba.

Ya kara da bayyana cewa, kwamitin gudanarwa na wani sabon masallacin Juma’a da ke bayan kwatas din babban bankin Najeriya (CBN), Abuja, ya nada shi ya jagoranci jama’a daga ranar Juma’a 8 ga Afrilu.

A cewarsa, “Kora ta ya bayyana yadda Najeriya take a yau. Mutane da yawa suna fakewa da addini don su aikata duk wani abu na rashin kyautatawa da kuma son zuciya.

Irin wadannan mutanen ba za su yi wata-wata ba sai sun ga sun kawar da mutane iri na wadanda ke magana da yawun talaka kuma suke fadin gaskiya ga shugabanni a madadin ‘yan Najeriya. “Wannan shi ne sakamakon mu saboda mun daidaita da jama’a kuma muna gane wahalhalunsu.

Da izinin Allah , zan fara sabon limanci a ranar Juma’a mai zuwa, saboda a matsayinmu na malamai, muna bukatar hanyar fadakarwa. “Akwai Masallacin Juma’a da muka gina a bayan kwatas din CBN a Abuja, yanzu ni zan dinga limanci a can.”

Related posts

Leave a Comment