Matsalar Tsaro: Da Yiwuwar Mu Dauko Sojin Haya Daga Waje – El Rufa’i

Rahoton dake zuwa mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya lashi takobin yin hayar sojoji daga kasashen ketare don su taya yaki da ‘yan ta’adda bayan harin da suka kai wa jirgin kasa a Kaduna ranar Litinin.

Ya kuma lissafo jihohi 4 na yankin arewa maso yamma, inda ya ce akwai yuwuwar su bi sahun shi. Jihohin sun hada da Zamfara, Kebbi, Katsina da Sokoto.

El Rufa’i ya ce zasu dauki wannan matakin ne matsawar gwamnatin tarayya bata dauki wani matakin a zo a gani ba a yankin.

El-Rufai ya shaida wa manema labaran cikin gidan gwamnati hakan, bayan ya kai wa shugaba Muhammadu Buhari ziyara har fadarsa don sanar da shi batun sabbin hare-heren.

“Meyasa har yanzu jami’an tsaro basu je sun halakasu ba? Ina sojojinmu? Meyasa suka yi wannan aika-aikar? Shi yasa na kawo wa shugaban kasa wannan ziyarar kuma in har ba a dauki mataki ba, mu za mu dauka.

“A matsayin mu na gwamnoni wajibi ne mu kula da rayukan mutanenmu. zamu nemi taimakon sojoji daga kasashen waje in har sojojinmu suka gaza, wallahi abinda zamu yi kenan.”

Related posts

Leave a Comment