Rundunar ?an sanda a Jihar Kano na shirin cafke wani shahararren mai sharhi kan al’amuran siyasa, Bashir Gentile, a kan zargin sukar gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, a wasu shirye-shiryen rediyo.
Bashir Gentile dai na hannun dama ne ga tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau, kuma mai taimaka wa shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan a halin yanzu.
An ruwaito cewa bayan yunkurin kama Gentile ya ci tura, a yanzu rundunar ?an sandan ta gayyace shi domin ya amsa tambayoyi kan karar da aka shigar a kansa.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ?an sandan, SP Abdullahi Kiyawa, ya ce ba shi da masaniya a kan gayyata ko shirin kama Bashir Gentilen.
Sai dai kuma SP Kiyawa, ya ce zai kara yin bincike kan lamarin.
A baya-bayan nan dai da dama daga cikin masu sukar gwamnan suna fuskantar tuhuma a gaban Alkalai bayan ‘yan sanda sun kama su.
Daga cikin masu sukar gwamnatin da a ka cafke sun ha?a da Mu’az Magaji da kuma Abdulmajid Danbilki Kwamanda, wanda a halin yanzu ya na gidan yari, sakamakon kasa cika sharu??an beli da a ka gindaya masa.
