Labarin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar Imam Muhammad Hashim, Limamin Babban Masallacin Juma’a na GRA Katsina ya ajiye mu?amin limancin saboda zai tsaya takara.
A wasi?ar ajiye limancin da ya rubuta, mai ?auke da kwanan watan 24 ga Maris, Mallam Hashim ya yi addu’ar Allah Ya rubuta masa ayyukan alherin da ya yi a cikin ayyukansa.
Wani ?angare na wasi?ar, na cewa: Ni Muhammad Hashim (Liman) na aje mu?amina na limancin Babban Masallacin Juma’a na GRA saboda tsaya wa takara da zan yi.
“Ina fatan Allah SWT ya rubuta mana ayyukan mu na alheri a cikin ibadun mu da mu ka gabatar, ya yafe mana kura-kuren mu Amin.
A cikin wasi?ar, mai ?auke da sa hannunsa, Hashim ya nemi yafiyar ‘?an kwamitin masallacin da ma al’umma baki ?aya.
