Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gabanin zaben 2023, malaman addinin Kirista na Arewa sun shirya gudanar da wani katafaren taron addu’o’i na mutum miliyan daya domin rokon cikar burin jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu.
A wani rahoto da Sahara Reporters ta fitar, kungiyar ta bayyana cewa a karshe burin tsohon gwamnan na jihar Legas na iya rugujewa idan ba tashi tsaye da addu’o’i ba.
Bishop Sunday Garuba, wanda ya jagoranci malaman ya bayyana cewa Allah ne ya umarce su. Ya ci gaba da cewa burin na Tinubu zai samun cikas daga miyagun da basu son alheri ga kasar nan.
Yayin da yake bayyana cewa Tinubu ne shugaban kasa na gaba da zai gaji Buhari, Garuba ya jaddada mahimmancin taron addu’ar ta kwana daya da suka shirya.
Malamin ya kuma bayyana cewa za su hada karfi da karfe domin karfafa muradin da Tinubu ke da shi domin amfanin Najeriya baki daya.
“A kasa da shekara guda, sabon shugaban kasa zai bullo don samar da wani sabon tsari ga al’umma. Bayan shafe sama da watanni uku muna addu’a da azumi da yawa, an bayyana mana cewa Bola Ahmed Tinubu ne jagoranmu na gaba.
