2023: ‘Yan Takarar Shugaban Kasa Daga Arewa Za Su Fitar Da Mutum Guda

Daga Adamu Shehu Bauchi

‘Yan takarar shugabancin Najeriya a zaben 2023 wanda suka fito daga yankin arewa sun kudiri aniyar fitar da dan takara daya tilo.

Hakan ya biyo bayan wata doguwar tattaunawa da suka yi a ranar lahadi a gidan gwamnatin Jihar Bauchi, yayin da suke ma manema labarai bayanin makasudin wannan doguwar tattaunawa, sunce suna tunanin su goyi bayan guda daya daga cikinsu.

‘Yan takarar dai wadanda suka hada da Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed da takwararsa na Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, kana da tsohon Shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki, da tsohon mataimakin Gwamnan zamfara da wasu masu ruwa da tsaki duk a wajen tattaunawar

Da yake jawabi wa manema labarai wanda ya jagiranci tattaunawar Bokola Saraki, yace irin wannan tunani Yana bukatar sadaukarwa da kuma jajircewa a cewar sa yanzu Najeriya ce a gabansu domin abubuwa sun tabarbare, suna so ne su shawo Kan matsalar in suka karbi mulkin kasan a zaben 2023.

Yace suna neman su kawar da bakin wahalar da Yan’Najeriya suka samu kansu a halin yanzu.

Tsohon shugaban Majalisar, ya sake cewa kan ‘yan siyasa da ‘yan takara su dauka zaben su da ake yi domin su kadai ne , ana zaben mutum ne domin ya zama silar sauya rayuwar al’umma, da kuma ci gaba mai dorewa a kasa baki daya.

Har-ila yau, yace ?asan nan ta shiga rudani, a cikin gwamnatin dake mulki a halin yanzu, a cewar shi sun kasa cika alkwarrun da suka dauka, yanzu mu ‘yan takarar PDP zamu kawo karshen wahalar da ake ciki in har muka sake samun damar jan ragamar shuganacin Najeriya.

Daga karshe sun ce zasu tuntubi Wazirin Adamawa Tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abaubakar don jin ta bakinsa kan wannan batu nasu daga arewacin Najeriya, a cewarsa tun da kasa suke so suyi wa aiki.

Related posts

Leave a Comment