Oyo: Mamu Ya Dirka Wa Matar Liman Ciki

Rahotanni dake shigo mana daga Ibadan babban birnin jihar Oyo na bayyana cewar Alhaji Lukman Shittu, wani malamin addinin musulunci a ya yi zargin cewa wani daga cikin wadanda suke sallah a masallacinsa ya ?irka wa matarsa ciki.

Ya yi wannan zargin ne yayin da ya ke bayani ga kotun kwastamare Grade A da ke zamanta a Mapo, Ibadan, babban birnin jihar ta Oyo.

Shittu, wanda matarsa ta yi kararsa na neman saki, ya shaida wa kotun cewa matarsa tana bin mazaje kuma ta haifi ?a?a uku da bai da tabbas nasa ne.

Nan take bayan sauraron wannan ikirarin, alkalin kotun S.M. Akintayo ya bada umurnin su tafi asibiti su yi gwajin ?wayar hallita ta DNA don sanin idan Shittu ne mahaifin ya’yan ko ba shi bane.

Alkali ya ce matar da mijin su hada kudi su biya gwajin DNA Akintayo ya ce: “Shittu da Fisayo za su hada ku?i su biya gwajin DNA ?in kuma za a tura wa kotu sakamakon gwajin kai tsaye”.

Kotun ta dage cigaba da shari’ar zuwa ranar 2 ga watan Mayu domin gabatar da sakamakon DNA.

Tunda farko, Shittu ya shaida wa kotu cewa matarsa ta fara tu?a zu?e?iyar mota jim ka?an bayan ta bar gidansa a 2021. Ya ce: “Duk da cewa Fisayo tana alfahari cewa ?an uwanta ne ya bata kyautan motar.

Binciken da na yi ya nuna min cewa, mutumin da suka dade suna ba?ala tare ne ya siya mata motar. “Fisayo ta fara rashin ji ne bayan na gaza bata ku?i ta karbi hayan shago. Daga nan, ta fara dawowa gida latti kuma na fa?a mata zan rufe ta a gida idan ta sake yin hakan.”

Amma, sai Fisayo ta kwashe kayanta daga gida na tare da yaran uku. “Ta canja wa na karshen makaranta ba tare da sani na ba, sauran biyun kuma sun ce daga yanzu sun daina ?auka na a matsayin mahaifinsu.

“A watan Ramadan da ya gabata, na gayyaci ?an mu na biyu ya zo wuri na amma ya ?i. Shima na farkon ya ?i zuwa gida na a lokacin da suka samu hutun makaranta.

Ko ka san cewa dadiron na Fisayo a masallacin da na ke limanci ya ke sallah?”

Fisayo ta yi zargi cewa Shittu yana neman mata kuma ya yi barazanar halaka ta da farko, Fisayo wacce ta shigar da karar, mai zaune a Odo Ona Elewe a Ibadan, ta ce mijinta ba shi da halaye masu kyau kuma barazana ne a gare ta.

“Shittu ya ru?e ni na kar?o bashi daga banki da sunan zan bude shago ba tare da na biya ba. Domin ya samu kawo mata gidansa, Shittu ya yi barazanar zai da?a min wuka idan ban bar gidansa ba. “Bayan haka, ya kan kowa mata daban-daban gidan mu na aure.

“Bugu da ?ari, Shittu ya rushe shagon da na gyara da ku?i na don kawai kada in yi kasuwanci. “Yana zagi na da sunaye daban-daban kuma ya taba cewa ‘?a?an mu ba nasa bane. “Duk da cewa ‘yan uwan mu sun shiga tsakani, amma na bar gidansa domin in tsira.”

Related posts

Leave a Comment