Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar bayan shafe akalla kwanaki 12 a kasar Burtaniya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya.
Shugaban ya tafi birnin Landan kusan makwanni biyu da suka gabata domin ganawa da masu duba lafiyarsa kamar yadda ya saba a duk shekara.
Shugaban ya dawo gida a ranar Juma’a, inda ya samu tarbar wasu daga cikin jiga-jigan gwamnati a fadarsa da ke Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewar jirgin shugaban kasan ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ne da misalin karfe 7.09 na dare.
