Neja: Izala Ta Share Wa ‘Yan Gudun Hijira Hawaye

Rahotanni daga Minna babban Jihar Neja na bayyana cewar Kungiyar Izala ta tallafawa ‘yan gudun hijira a kananan hukumomi 13 dake fama da matsalar tsaro a Jihar.

Kungiyar ta bada wannan tallafi ne ga yan gudun hijira dan rage masu radadin da suke fama dashi na rayuwa sakamakon fitintinun ‘yan ta’adda da ya raba su da garuruwan su.

Shugaban kungiyar ta jahar Neja Alh Abdullahi Musa Mai Radiyo Shi ya jagoranci kaddamar da wannan gagarumin aiki.


Kayayyakin sun ha?a da
Shinkafa buhu 113
Semovita 100
Wake buhu 10
Masara buhu 5
Dawa buhu 1
Taliya Caton 105
Madara Caton 100
Sugar buhu 20
Indomi 210
Manja Jarka 20
Mangyada 50
Tabarma 250
Atamfa turmi 203
Sai kayan sawa na maza da mata

JIBWIS NIGERIA

Related posts

Leave a Comment