Buhari Ya Mika Ragamar Mulki Ga Osinbajo

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya ce mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ne ke jagorantar ?asar.

Shugaban ya fa?i haka ne a Abuja lokacin da zai taka jirgi zuwa London a ranar Lahadi.

Kafin ya hau jirgi, Buhari ya fa?a manema labarai a Abuja cewa mataimakin shugaban ?asa ne zai ci gaba da tafiyar gwamnati idan baya nan, kamar yadda tsarin mulki ya yi tanadi.

Buhari ya tafi London ne domin ganin likitocinsa, kuma fadar shugaban na Najeriya ta ce, zai shafe tsawon mako biyu a can.

Buhari ya ce rashinsa ba zai shafi ayyukan gwamnati ba, domin yana sane da duk wani abin da ke faruwa ko da kuwa baya nan.

Related posts

Leave a Comment