Tashin Bam: Gwamnatin Kaduna Ta Bukaci Jama’a Da Taka Tsan-Tsan

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin jihar ta yi kira ga jama’ar jihar su sanya ido sosai kan abubuwan fashewa da ?an ta’adda ke ajiyewa a wuraren taruwar jama’a.

Cikin wata sanarwa da ma’aikatar tsaro ta jihar ta fitar ta bayyana cewa gwamnatin ta ce hakan ya biyo bayan binciken da hukumomin tsaro ke ci gaba da yi a kan zargin cewa ?an ta’addan na neman cutar da jama’a ta hanyar binnewa, da kuma ajiye abubuwan fashewar a makarantu, da asibitoci, da otal-otal, da gidajen cin abinci, da wuraren shakatawa, da wuraren ibada.

Sanarwar ta ?ara da cewa hukumomin tsaro suna aiki don tabbatar da cewa babu wanda aka cutar a cikin jama’a.

Ta kuma yi kira ga jama’a su bayar da rahoton duk wani mutum ko wani abu da aka gani ba a yarda da shi ba.

Related posts

Leave a Comment