Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun sake samun gagarumar nasara a kokarinsu na kakkabe yan ta’adda da miyagu a yankin arewa maso gabashin kasar.
A yanzu haka, mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram da iyalansu 41 sun mika wuya a ranar Litinin, 21 ga watan Fabrairu.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na Twitter a ranar Talata, 22 ga watan Fabrairu, ta bayyana cewa wadanda suka mika wuya sun hada da maza 11, mata 22 sai yara takwas.
Rundunar sojin ta rubuta sanarwar kamar haka: “Aikin kakkaba da ke gudana a yanzu ya sake samun gagarumin nasara yayin da mayakan Boko Haram da iyalansu 41 da suka hada da maza 11, mata 22 da yara 8 sun mika wuya ga dakarun Bataliya ta 144 da ke kauyen Dissa na jihar Borno a ranar Litinin, 21 ga watan Fabrairu.”
