Tinubu Ne Silar Matsalar Da Jihar Osun Ke Ciki – Ministan Cikin Gida

Labarin dake shigo mana daga Jihar Osun na bayyana cewa Ministan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola ya soki lamirin jagoran APC Bola Tinubu, ya ce ya ?ora masu Gwamna bara gurbi a Jihar Osun.

Da ya ke wa taron magoya bayan APC jawabi a garin Ijebu-jesa, Aregbesola wanda shi ya yi gwamna tsawon shekaru takwas sannan ya sauka Gwamna Gboyega Oyetola ya gaje shi, ya ce ya amince da Oyetola ya zama gwamna ne bayan Tinubu ya bada shi a matsayin wanda ya ke so ya gaje shi, kuma ya yi al?awarin zai ?orawa kan ayyukan raya ?asa da Aregbesola ya kafa a Osun.

“Amma Oyetola na hawa a 2018 kujerar gwamna, sai ya kauce, ya saki hanya, ya shiga daji kuma ya karya al?awari.”

Daga nan sai Aregbesola ya ce “kamar yadda Tinubu da mutanen sa su ka yi wa tsohon Gwamnan Legas Akinwunmi Ambode saboda ya saki hanya, su ma a Jihar Osun haka za su yi wa Oyetola tunda ya saki hanya.”

“Kamar yadda aka yi a Legas, mu ma a Osun za mu yi amfani da ?uri’u mu watsar da mugun irin da aka dasa mana, maras cika al?awari.” Inji Aregbesola.

“Ku je ku shaida masu mu ke da jam’iyyar nan. Kuma mu ne ‘yan Afenifere na gidi. Mu ke ?yan?yasar Awolowo da Bola Ige.

“Wannan jam’iyya APC ta mu ce, mu ba ‘ya’yan bora ba ne.”

Can da jawabi ya yi zafi, Aregbesola ya fito ?uru-?uru ya na ragargazar Tinubu da Gwamna Oyetola, har ya na yi masu wa?a da Yarabanci, ya na cewa, “adabo da gayyar tsiya.”

“Yanzu mun dawo gida domin mu ?ora jam’iyyar mu a kan hanya, ta yi saitin tafiya sosai a kan mi?a??ar hanya.

“Mun bi mutumin nan, mun yi tsammani nagari ne. Wasu ma har ?o?arin fitar da mu daga Musulunci su ka yi don mun bi shi. Mun ri?e shi amana babu sharri, amma ba mu sani ba ashe shi sharri ya ke ?ulla mana.

“Mun kai shi inda Ubangiji bai kai shi ba. Shi kuma ya ri?a ?aukar kan sa kamar wani ubangijin bautar mu.

“Mu kuma mun rantse sai mun tozarta duk wani da ya ?auki kan sa tamkar ubangiji.

“Mu muka gina wannan jam’iyya bayan mun sha wahala da gumi har wasu da dama mun rasa su. Mun hau mulki ranar 27 Ga Nuwamba, 2010. Mun yi mulki shekaru takwas, a bisa adalci kamar yadda Allah ya ce mu yi adalci. Kuma jama’ar Osun sun ji da?in mulkin mu.”

Related posts

Leave a Comment