Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na ya kasar Belgium a ranar Talata don halartar taron ha?in gwiwa tsakanin ?ungiyar ha?in kan Afirka ta African Union (AU) da takwararta ta Tarayyar Turai (EU).
Taron wanda zai gudana a birnin Brussels daga 17 zuwa 18 na Fabarairu, inda shugabannin nahiyoyin biyu za su tattauna matsalolin da ke faruwa a yankunansu.
Wata sanarwa daga fadar shugaban ?asa ta ce ana sa ran Buhari zai koma gida ranar Asabar. Ta ?ara da cewa shugaban zai yi amfani da damar wajen tattauna sauran al’amura da wasu ?asashe.
Abubuwan da shugabannin za su tattauna sun ha?a da batun ilimi da sauyin yanayi da makamashi da zaman lafiya da harkokin mulki da harkokin tattalin arziki.
