Fargabar Korona: Da Yiwuwar A Sake Kulle Najeriya


A daidai lokacin da ‘?an Najeriya ke kokarin kai komo wajen neman abin dasu saka a bakin salati, da kuma zaman dardar da ake yi na hare-haren ?an bindiga da ya addabi mutane a Najeriya, hukumar NCDC ta bayyana cewa akwai yiwuwar sake garkame kasar nan idan aka ci gaba da samun yawan wa?anda suka kamu da Korona a kasar nan.

Shugaban hukumar NCDC, Ifedayo Adetifa,ya bayyan cewa Korona ta yi ?amari yanzu a kasar nan akwai yiwuwar gwamnati ta ?au sabbin matakai a kasar nan.

A karon farko tun barkewar Korona a watan Faburairun 2020 Najeriya ta samu sama da mutum 4000 da suka kamu da cutar a rana ?aya

” Mutane sun yi watsi da matakan kariya da a ka saka da suka ha?a da wanke hannaye, mulka man tsaftace hannaye, saka takunkumin fuska da yin nesa da juna, sannan kuma da rage cunkoso da taruka.

” Ba mu bukatar ace an kai ga har sai ?asa ta ?auki matakin da za a muzanta wa mutane amma kuma kiwon lafiyar mutane shine a gaban gwamnati.

Sai dai kuma ba a nan ne gizo ke saka ba domin wasu kwararru da suka tattauna da PREMIUM TIMES game da wannan niyya ta gwamnati sun ce haka nan dai gwamnati za ta ci gaba da hakuri da mutane amma saka dokar zaman Kulle ba zai yiwuba a Najeriya yanzu ba.

” Matsalolin da za a afka a ciki sun fi duk wani alfanu da za a samu idan aka garkame kasar.

Related posts

Leave a Comment