Sarkin masu bautar shai?an’ na Najeriya Simon Odo wanda shi ne mutumin da ya auri mata 57 ya rasu yana da shekara 74.
?ansa Uchenna Odo ne ya tabbatar wa BBC da lamarin inda ya ce mahaifinsa ya rasu ne a ranar Talata da dare bayan gajeruwar rashin lafiya.
Simon Odo wanda asalinsa ?an Jihar Enugu ne ya shahara ne a kudancin Najeriya a harkar bokanci da bautar shai?anu.
A yayin wata hira da BBC a bara, marigayin ya ce ya auri mata 57 kuma bai san iyakar ?a?an da matansa suka haifa ba haka ma jikokinsa.
Ya kuma bayyana wa BBC cewa ya gaji bautar shai?an ne daga iyayensa da kakanni.
