Borno: Dakarun Soji Sun Hallaka Mayakan ISWAP Masu Yawa

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar kashe a?alla maya?an ISWAP 24.

Kafar watsa labarai ta PRNigeria ta ruwaito cewa maya?an sun gamu da ajalinsu ne a yayin da suka yi ?o?arin kai hari a wani sansanin soji da ke Rann, wanda gari ne da ?an ?ungiyar Boko Haram suka lalata a baya a jihar Borno.

Sai dai sojin ?asar sun rasa sojoji biyar yayin wannan bata-kashin da aka yi tsakanin ?an ISWAP ?in da kuma sojojin rundunar Operation Hadin Kai.

Har yanzu ana samun hare-haren ?ungiyoyin masu i?irarin jihadi a arewa maso gabashin ?asar.

Ko a cikin watan Nuwambar da ya gabata sai da ?an ISWAP din suka kashe wani janar ?in sojin Najeriyar a jihar Borno da kuma wasu ?ananan sojoji yayin wata bata-kashi da yan tayar da ?ayar bayan.

Related posts

Leave a Comment