Bauchi: Masu Bukata Ta Musanman Sun Koka Rashin Ruwa A Makewayi

Daga Adamu Shehu Bauchi

Masu Bukata ta musamman a Jihar Bauchi sun Koka ma gwamnati da masu ruwa da tsakin ta fannin tsaftar jiki da su samar masu da ruwa a yan’kunan su domin saukaka masu amfani biyan bukatarsu ta yadda ba sai sun sha wahalan neman ruwan ba a wuri mai nisa.

Sunyi wan nan korafin ne a wajen taron bikin tunawa da ramar wanke hannu na duniya da aka yi a Jihar Bauchi na shekarar 2021.

Shugaban Kungiyar masu fama da ciwon da ya shafi kashin baya na Jihar. Malam Yahaya Isma’il, wan nan rana ta musamman ce a gurinsu masu Bukata ta musamman domin, shine bangaren dake ci musu tuwu a kwarya, yace Gwamnati ya kamata ta Kara kaimi sosai domin tallafa ma su ta fannin samar da wurare na musamman da zasu rika samun ruwa ba tare da sunsha wahala ba.

A cewarsa dukkan tsaftar jiki baya cika sai da ruwa musamman hannu da sauran bangaren jiki don tabbatar da tsaftar dole ne sai Gwamnati ta tashi haikan, “shi tsaftace hannu da kuma jiki gaba Daya ya ta’allaka ne da amfani da ruwa, Ina kira ga mahukunta su samar da ruwa ga al’umma, tare da kulawa da masu bukata ta musamman wajen amfani da ruwa a makewayen mu da wajen wanke hannuwa, anayi mana su yadda basai mun sha wahala ba”

Asama’u Yahaya, anat tsokacin Kan wan nan rana tace mahukunta su rika cibgaba da wayar ma masu bukata ta musamman kai a cikin lungu da sako a maimakon a rika taro a wani wuri wanda baza su iya zuwa ba domin fahimtar dasu kan muhimmanci tsaftar jiki.

Yahaya ta kara da cewa, “rana ce da take da muhimmanci a rayuwarmu, muna so muga anje wurin da masu bukata ta musamman suke a rika wayar mana da kai, saboda inganta rayuwarmu ba Wai kawai Gwamnati ta ta’allaka a guri guda ba, a Bauchi a kwai wurare kaman Bayara aje a wayar masu da kai su san meye tsaftar jiki”.

Shugaban hukumar Samar da ruwan sha a karkara injiniya Garba Magaji, a wajen taron yace suna kokari sosai ta wajen samar da ruwa a wurare da dama a kauyoka har da wuraren masu bukata ta musamman a dukkannin fadinmjihar Bauchi, yace amma matsalar shine su zasu nada ruwa amma kula da ruwan do yakai wani lokaci Mai tsawo, baya hannun su dole ne sai masu amfani da ruwan bada tasu gudummawar ta wajen kuka da lura sosai daga lalacewa.

Kana injiniyan ya kara da cewa, “;tun lokacin da muka samu tallafi daga (Unicef da Wateraid) munsa masu bukata ta mussaman a cikin, Kamar yadda na gaya maka suma sai sun kula ba mine zamu rika zuwa muna kula masu da kayan da muka basu ba dole sune zasu kula da kayayyaki irin wadan nan”, ya jaddada.

Ya ce in Kuma sun’sami matsala ne ta wajen amfani da su to zasu iya sake tallafa masu ta wajen gyaransu don ci gaba da amfanin kansu, domin su samu saukin tsaftace jikin su, su masu bukata ta musamman.

Related posts

Leave a Comment