Hukumar Za?e ta ?asa (INEC) ta bada hasashen cewa mai yiwuwa ne a yi wa sababbin jam’iyyun siyasa rajista kafin manyan za?u??ukan shekarar 2023.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bada wannan hasken a wurin babban taron shekara-shekara na jam’iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki wanda aka yi a Abuja.
Kalamin ya fito ne a cikin jawabin da wakilin sa a taron, Babban Kwamishina kuma shugaban Kwamitin Tuntu?a a hukumar, Dakta Adekunle Ogunmola, ya gabatar a taron mai taken: “Jam’iyyun Siyasa da ?orewar Dimokira?iyya a Nijeriya: Nuna Al?ibla Ga Manyan Za?u??ukan 2023.”
Bugu da ?ari, kafin za?u??ukan na 2023, ahugaban hukumar ya bayyana damuwa kan yadda jam’iyyun siyasa su ke gudanar da harkokin su, ya ce ya kamata su yi gyara.
?aya daga cikin matsalolin su da ya nuna su ne rashin bin tsarin dimokira?iyya a cikin jam’iyya, ninanci, ware mata da na?asassu da kuma matasa.
A yayin da shugaban ke nuna yiwuwar yi wa ?arin jam’iyyu rajista kafin lokacin manyan za?u??ukan, ya kuma bayyana cewa hukumar na sa ran cewa matsalolin da ke akwai a ?asar nan ba za su zama barazana ga aiwatar da manyan za?u??ukan 2023 ba.
Ya ce, “Ina ganin cewa irin wannan babban taron ya na da muhimmanci a wajen yadda mu ka yi nazarin yanayin siyasar ?asar nan ta hanyar yadda jam’iyyun ke taka rawar su, kuma mun gano wasu matsaloli da mu ke bu?atar a warware, kuma wannan shi ne dalilin shirya irin wannan taron, saboda abin da su ka samar a nan a yi amfani da shi wajen gyara tsarin siyasa.ADVERTISEMENT
“Don haka, babu wani abu a tsarin mu da ya ce kada mu ci gaba da yi wa jam’iyyun siyasa rajista in dai sun cika dukkan ?a’idoji. Saboda haka dukkan ?ungiyoyin da ke so a yi masu rajista, a shirye INEC ta ke ta yi masu rajistar sai dai idan sun kasa cika ?a’idojin.
“Yardar mu dai na ga Allah, mun ta?a samun irin wannan yanayin a baya kuma mun samu damar magance shi kuma mu na fatan a wannan karon, za a yi za?u??ukan 2023 cikin nasara fiye da za?u??ukan baya.”
A nasa ?angaren, Darakta-Janar na Cibiyar Nazarin Tsare-tsare da Dabarun Mulki ta Nijeriya (NIPSS), Birgediya-Janar Chukwuemeka Udaya (ritaya), ya shawarci jam’iyyu da su gyara tsare-tsaren su wajen fa?a?a tare da rungumar membobin su wajen tafiya tare da mata da matasa.
A yayin da ya ke nuna wasu daga cikin matsalolin yanayin siyasar ?asar nan, Udaya ya ce jam’iyyu na bu?atar su gyara hanyoyin gudanarwar su don tabbatar da ?arin taka rawar mata da matasa.
Ya ce, “Akwai mishkiloli da yawa irin su tsarin dimokira?iyyar cikin jam’iyyu, ninanci; bu?atar ?arin taka rawar mata, bu?atar shigo da matasa; da bu?atar rungumar mutane masu fama da na?asa (PWDs), ba kawai a matsayin masu jefa ?uri’a ko membobin jam’iyya ka?ai ba har ma a matsayin shugabannin jam’iyyun siyasa da kuma a matsayin za?a??un wakilan jam’iyyun siyasa.”
Udaya ya kuma shawarci ‘yan siyasa da kada su kalli lamarin siyasa a matsayin a mutu ko a yi rai.
Ya ce, “Abin da mu ke so jam’iyyu su ?auka daga wannan taron ?ara wa juna sani shi ne kowane ?an Nijeriya ya rage rarrabuwar kan da ke akwai; akwai manyan rarrabuwar kai kuma ha??in jam’iyyu ne su ha?e kan ?asar nan, su ?ora ?asar a kan al?ibla da turbar za?u??ukan 2023.
“Al?iblar a bayyane ta ke, akwai al’amuran tsaro, akwai al’amuran tattalin arziki, kuma wa?annan su ne abubuwan da mu ke so su tattauna a kan su idan shekarar 2023 ta ?arato.”
An shirya taron ne don a samar da al?ibla game da za?u??ukan 2023 kuma a wayar da kan jam’iyyu game da 2023.
Wa?anda su ka shirya taron su ne NIPSS, tare da ha?in gwiwar Tarayyar Turai (EU); Cibiyar Shugabannin Jam’iyyun Siyasa da Cigaban Tsare-tsare (Parties Leadership and Policy Development Centre) da sauran masu ruwa da tsaki.
