Shugaban Ri?on Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa na Najeriya (NPA) Bello Koko, ya shiga cikin ?azamar ?amayamaya da ?a?ububar satar ku?a?en Najeriya ya na kartatar da su waje, inda ya ke sayen maka-makan gine-gine da kadarori a birnin Landan.
A ?ar?ashin wannan har?alla, ya ri?a yin shigar kare-da-fatar-akuya da sunan wasu kamfanoni biyu na Shell, ya ri?a dan?ara ku?a?en da ake sayen kadarori a Landan.
Gungun ‘yan jarida masu ya?i Da ?arayin ku?a?en gwamnati a duniya ne su ka banka?o wannan ?azamar har?allar da ake kira ‘Pandora Papers’.
Bello Koko tare da matar sa mai suna Agatha Anne Koko, sun yi amfani da wani kamfanin ?oye sirrin ma?arnata, Cook Worldwide and Alemin, su ka yi rajistar kamfani a asirce ta hanyar ?oye sunayen su, aka sa sunayen bige a matsayin masu kamfanin.
An ra?a wa kamfanin suna Coulwood Limited, mai rajista lamba 1487897.
An sake ?ir?irar wani kamfanin na bige mai suna Marney Limited a British Virgin Islands, mai lamba 1487944, duk a cikin 2008.
Wa?annan kamfanonin biyu an yi masu rajista duk a rana ?aya, 19 Ga Yuni, 2008.
Duk da Bello Koko ma’aikacin gwamnati ne, ya kasance daraktan kamfanonin, abin da ya sa?a wa Dokar Aikin Gwamnanti a Najeriya, Sashe na 5 da na 6.
Har?allar Bello na daga cikin har?alla miliyan 11.9 da Gamayyar ?ungiyoyin ‘Yan Jaridar Binciken ?wa?waf na Duniya (ICIJ) su ke ci gaba da fallasawa bayan sun banka?o su.
Jaridar PREMIUM TIMES ka?ai ce cikin wannan ?ungiya a jaridun Najeriya. Kungiyar ta ?unshi ‘yan jarida 617 daga gidajen jaridu 150 na ?asashen duniya.
Wa?annan ‘yan jarida sun shafe shekaru biyu su na bicike a cikin har?allar tare da bin diddigin hanyoyin da ake satar ku?a?en, binciko fayil-fayil ?in wasu shari’un da ake yi na wasu ?asashe daban-daban.
Wannan fallasar manyan ?arayin gwamnati ita ce mafi girma da ‘yan jarida su ka ta?a yi daga cikin ?asashe 117 na duniya.
Kadarorin Da Bello Koko Ya Saya Cikin Landan, A ?ar?ashin Mulkin Buhari:
Daga cikin kadarorin da Bello Koko ya saya Landan, har da wa?anda ya saya a Landan cikin 2017, lokacin da bai da?e da zama Babban Darakta a NPA ba.
Sauran kadarorin kuma ya saye su tsakanin 2008 zuwa 2012.
Da farko ya sayi gida mai Lamba 2, Liberty Court, 141, Great North Way, London.
Ya sayi gidan a ranar 20 Ga Okotoba, 2009, ta hannun dillalin FBN UK mortgage.
Ranar 23 Ga Yuli, 2012, ya sayi mai Lamba 62, Manton Road, Enfield, London.
An sayi ?aya fam 280,000, ?ayan kuma fam 275,000.
Bello Koko ya sake amfani da kamfanin Coulwood a wannan karo, ya sake sayen gidaje uku.
Akwai mai Lamba 62 Corner Mead, Hendon, (NW9 5RD) a ranar 25 Ga Nuwamba, 2008.
Sai gida mai Lamba 37, Redlands Road, Elfield da aka saya a ranar 16 Ga Agusta, 2011.
Lamba 14, Farady House, Aurora Garden, London, shi kuma an saye shi a ranar 3 Ga Mayu, 2017, a wannan gwamnati ta Mahammadu Buhari.
Na farkon an biya fam 205,000, sai na biyu fam 235,000. Sai kuma gidan Hendon da ya biya fam 350,000.
Na Aurora Garden kuwa da ya saya cikin 2017, ya biya lakadan fam 475,000.
Wannan kantamemen gini shi ne babbar kadara mafi girma da Bello Koko ya saya a Landan.
Kuma ya saye ta lokacin mulkin Buhari ?in nan, ya na aiki a Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa (NPA).
Kamfanonin har?allar Bello Koko na cikin wa?anda Hukumar Bibiyar Har?alla a Birtaniya (FIA) ta kafa wa idon mikiya a halin yanzu.
Kafin Bello Koko ya fara aiki a Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa, ya kashe fam miliyan 995,000 wajen sayen kadarori a Landan, tsakanin 2008 zuwa 2012 kenan.
Ba a san dalilin da ya sa ya ri?a sayen gidajen da sunan bogi, maimakon sunan sa na gaskiya ba.
PREMIUM TIMES ta aika masa da sa?on tes, domin jin ta bakin sa, har yau bai maido amsa ba.
A ranar 27 Ga Janairu, 2017, Hukumar Binciken Ku?a?en Har?alla (FIA) a Landan ta nemi ?arin bayanai dangane da ganin sunaye da kuma bayyanar masu kamfanonin da Bello Koko ke har?alla, tare da neman wasu ?arin bayanai daga gare su, amma aka yi ta dawurwura da dabur-dabur.
