Federico Chiesa ya taka rawar gani a tawagar Italiya a Euro 2020, amma sai a wannan karon yake fito da kansa a Juventus.
Mai shekara 23, shine ya ci Chelsea kwallon da ya bai wa Juventus maki ukun da take bukata ranar Laraba a Turin.
Wanda ya taka rawara gani a Euro 2020 har da cin Sifaniya kwallo a karawar daf da karshe, baya buga wasanni sosai tun bayan da koci Massimiliano Allegri ya sake karbar ragamar horar da kungiyar Turin.
Jinyar rauni da ya yi ta taka rawar gani, sai dai a wasu rahotanni a Italiya sun ce ba jituwa mai karfi tsakanin dan kwallon da kuma kocin.TALLAhttps://a183421adbde57cd686f600c60bb4725.safeframe.googlesyndication.com/safeframe/1-0-38/html/container.html
Tun farkon fara kakar bana an tambayi Allegri dalilin da ya harzuka da suka tashi 1-1 da AC Milan a Serie A, sai kocin ya ce ”Na umarce shi da yake zuwa da kwallo gidan abokan wasanmu a koda yanshe, Ya kamata ya kara sa lura ya kuma san a Juventus yake.”
Bayan da aka fara wasa da shi a karawa da Chelsea mai rike da Champions League, Chiesa ya nuna kwarewarsa da haska fitular shine magajin Ronaldo
Chiesa ya zama dan kasar Italiya na farko da ya ci kwallo a wasa hudu a jere a Champions League a Juventus, tun bayan bajintar Alessandro Del Piero a Nuwambar 1997.
