Rahotanni daga birnin Kano na bayyana cewar babban ?an Ganduje Abdulazeez Ganduje, ya tsere zuwa ?asar Masar tare da iyalinsa bayan ya tona asirin cin hanci da ake zargin mahaifiyarsa dashi.
Abdulazeez Ganduje ya kai mahaifiyarsa, Hafsat Ganduje kara a Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC, bisa zargin cin hanci da rashawa.
Dan gwamnan ya roki cewa wani dillali ya tuntube shi don taimakawa wajen saukake siyan wasu filaye a Kano tare da wasu daruruwan dubban dalolin Amurka da akalla sun kai Naira miliyan 35 a matsayin kudin kwamisho.
“Amma bayan watanni uku, (dillalin) ya gano cewa filayen da yake so kuma ya biya iyalan an raba su ga sauran masu siye sannan ya nemi a mayar masa da kudinsa.” Duk da cewa har yanzu matar Ganduje ba ta amsa gayyatar ba, amma majiyoyin tsaro sun ce za ta iya fukstar kamun jami’an EFCC tunda ba ta da kariyar kamawa da gurfanar da ita.
Majiyoyin kusa sun ce dan gwamnan ya gudu zuwa Masar nan da nan bayan ya shigar da karar don gujewa “fushin iyayensa”. Wata majiya ta ce: “Abdulaziz ya bar Najeriya zuwa Egypt tare da iyalansa kai tsaye bayan shigar da kara.
“Ya guji iyayensa kuma ya shiga duniya tun farkon rikicin.” An gagara samun wayar Abdulazeez ta lambarsa ta Najeriya don jin ta bakinsa.
