Katsina: Mata Mafarauta Sun Sha Alwashin Ganin Bayan ‘Yan Bindiga

Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar Kungiyar mafarautan Najeriya, NHC, reshen jihar Katsina da ke arewa maso yamma ta yanke shawarar taimaka wa gwamnatin jihar yaki da ta’addanci a fadin jihar.

Hajiya Ummah Dauda, mataimakiyar kwamanda janar na kungiyar, ta jagoranci sauran ‘yan kungiyar zuwa ofishin sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Muhammad Inuwa, inda ta bada wannan tabbaci.

Yayin jawabi a ofishin Sakataren Gwamnatin Ummah ta bayyana cewa a cikin kungiyar mafarautan za su iya sadaukar da ran su wurin kawo karshen ta’addanci a jihar. Kamar yadda ta ce: “A matsayin mu na mafarauta, mun san daji kwarai don haka mu yafi dacewa a ce mun yaki ‘yan ta’adda a jihar.

Da yawan mu muna da tsarin da harsashi ba zai ratsa mu ba. Kuma mun samu horarwa wurin yaki. “Hakan ya sa na ke rokon gwamnati ta yi wannan tafiyar da mu don kawo karshen ta’addanci a jihar nan.

“Akwai mafarauta a kalla 100 a ko wacce karamar hukuma. Kuma akwai kananun hukumomin da sun fi mutane 100 a can. “Wasu daga cikin mu za su iya kama ‘yan ta’adda kuma su mika su ga jami’an tsaro don yi musu hukunci. “Don haka muke bukatar gwamnatin jihar nan ta bamu dama don a shirye muke mu kamo su ko a yanzu.”

Related posts

Leave a Comment